Ƴansanda sun yi awon gaba da Dino Melaye daga asibitin da yake jinya

0 303

Jami’an ƴansanda dake rufe da fuskokinsu sunyi awon gaba da Sanata Dino Melaye daga kan gadon asibitin da yake kwance ya zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Tun lokacin da aka kama shi a makon da ya wuce Melaye ke kwance a asibitin ƴansanda dake Garki bayan da aka rawaito ya fadi a hedkwatar rundunar ƴansandan Najeriya dake Abuja.

Sanatan ya mika kansa ga jami’an ƴansanda bayan da suka shafe kwanaki takwas suna yi wa gidansa dake Abuja kawanya.

Ƴansanda na zargin sanatan da hannu a aikata kisan kai inda suke zargin magoya bayansa da harbe wani jami’in ɗansanda mai suna Danjuma Saliu.

Duk da cewa Melaye na kwance a asibiti tun bayan da aka kama shi ƴansanda sunce kalau yake kuma zai iya tsayawa gaban kotu ya fuskanci shari’a.

Amma wata majiya ta shedawa jaridar The Cable ranar Juma’a cewa jami’an tsaron sun dauke Melaye ne duk da shawarar da kwararru akan harkar lafiya suka bayar kan kada suyi ka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.