A Yau Ne Shugaba Muhammadu Buhari Ke Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa

0 277

– Yau 17 ga watan Disamba ne yayi daidai da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya cika shekaru 76 a duniya.

– Manyan shugabannin Najeriya sun fara aika sakon taya murna ga shugaban kasar

– Jonathan ya ce Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa Najeriya hidima.

A ranar yau 17 ga watan Disamba ne yayi daidai da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya cika shekaru 76 a duniya. Tuni a dai manyan ‘yan Najeriya suka fara taya shugaban kasar murnar, tare da addua’r Allah ya albarkaci rayuwarsa da kara masa lafiya. 

Sai dai kuma da yawa sun yi amfani da damar wajen janyo hankalinsa ga halin matsi da kuncin rayuwa da ‘yan kasar ke ciki.

Yayin da manyan yan Najeriya kamar su, tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha suka fitar da sakonnin yi wa shugaban murnar zagayowar ranar haihuwar sa suka kuma yi masa addu’ar karin lafiya, talakawan Najeriya ma sun yi amfani da shafukan sada zumunta kamar su Facebook wajen yi masa fatan alkhairi. 

Jonathan ya ce, Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa Najeriya hidima kasancewa ya yi aikin soja inda ya rike mukamin Gwamna, Minista, Shugaban kasa na mulkin soja da na farar hula da yake yi a yanzu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.