A Zaben 2019: INEC zata horar da sama da ma’aikata dubu 800

0 258

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce zata horar da sama da ma’aikata dubu  800 a babban  zaben shekarar 2019. Shugaban cibiyar horar da ma’aikatan zaben Prince Solomon Adedeji Soyebi ne ya sanar da hakan.

Prince Soyebi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin horarwar kwana biyu da aka yi wa ma’aikatan zaben, don shirya wa babban zaben 2019.

Soyebi ya kara da cewa, ya zama wajibi ga hukumar zaben ta shirya tsaf kasancewar saura kwana 60 a gudanar da babban zaben 2019

Leave A Reply

Your email address will not be published.