Abokin Miji Na Complete

0 995
ABOKIN MIJI NA COMPLETE HAUSA NOVEL.

B’angaren su Husna kuwa hiran su suke sosai da Hafsat,  itama Hafsat ta sake jiki da Husna dan taji tanason ta.

  Husna ce tace
“Anty Hafsat me kike son kici zan shiga kitchen na d’aura abinci.”

“Aa Husna komai kika dafa zanci dan bana sha’awan komai.”

  Ta tashi zata shiga kitchen kenan sai gasunan sun shigo Farooq ya bud’e baki zaiyi magana amman Yusuf ya rigashi da cewa
“Aa Husna ina zaki naga kin tashi?”

  Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace
“Kitchen zan shiga d’aura girki.”

Farooq ne yace
“Yauwa yayi dai-dai muje muyi girki kai kuma sai Ka zauna wajen matar ka kafin mu gama” yana k’arasa maganar ya ja hannun Husna sukayi kitchen.

  Shikuwa Yusuf wani bakin ciki ne ya lullu6eshi daman shi yazone dan Husna kuma gashi ta tashi wanne hanya zaibi dan ya dawo da su.

  Ai kuwa a take wani abu ya fad’o masa da sauri ya mik’e shima ya shiga kitchen d’in.

  “Haba dan Allah ya munzo gidan ku zaku shiga kitchen Ku barmu a parlour.”

  Husna kam har ta tsorata dan batayi tsammanin mutum ba.

  Farooq ne yace
“To Idan bamu girka muku abinci ba ya zamuyi kenan?” Ya tambaye shi.

  “Abu mai sauki anjima kaje kasiyo mana.”

  Da k’arfi Farooq yace
“Abincin siya!
Sanin kanka ne kasan bana cin abincin siyarwa Yusuf dan Allah kaje Ka zauna yanzu zamu gama mu dawo.”

  Zuciyar shi cike da Kuna ya dawo ya zauna yana kullah abinda zai shirya.

WhatsApp: 08161892123
Domin karanta Cikakken wannan Littafi sai Ku Shiga kasan nan Download.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.