An Bayyana Sunan Ganduje A Matsayin Wanda Ake Zargi Da Amsar Cin Hancin Dala Miliyan Biyar

Ganduje

0 191

Hukumomin tsaron Nijeriya na kan gabatar da bincike game da wasu faya-fayan bidiyo da ke nuna gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na amsar cin hancin Dalar Amurka miliyan biyar.

Tarin ‘yan kwangilar da suka tattauna da jaridar DAILY NIGERIAN k’ark’ashin yarjejeniyar k’in ambatar sunansu sun ce gwamnan da kansa yake amsar cuwa-cuwar kashi 15 zuwa 25 na kowanne aiki da aka gabatar a jihar.

Wasu majiyoyi da ke da kusanci da sha’anin sun ce Shugaban k’asa Muhammadu Buhari ya umarci wasu hukumomi guda biyu da su rubuta rahoto sannan su damk’a masa a cikin gaggawa.

Majiyoyin sun ce rahoton ya k’unshi bincike a kan hoton bidiyon da kuma muryar da ke tashi a ciki, sannan kuma su rubuta shawararsu game da lamarin ga Shugaban k’asa.

Wata majiya mai tushe daga fadar shugaban k’asa ta gaya wa DAILY NIGERIAN cewar Shugaban k’asa zai ɗau mataki a kan rahoton da zarar hukumomin guda biyu sun damk’a masa rahoton.

“Da fari an nuna wa Shugaban k’asa bidiyon a babbar talabijin. Ranshi ya yi matuk’ar ɓaci bayan ya ga faifan.

“Na yi imanin zai ɗau mataki a cikin lokaci,” majiyar ta faɗa.

Shirin tsige gwamnan, wanda yake k’ok’arin tazarce a k’ark’ashin tutar jam’iyar APC ya yi nisa a ranar da Shugaban k’asa ya yi bincike game da dukkan matakan da za a iya ɗauka.

Wasu masu bayar da fashin-bak’i game da lamarin sun ce tsaf ‘yan majalisar dokoki na jihar zasu yi biyayya ga rok’on Shugaban ‘kasa kan tsige gwamnan sakamakon fitar faya-fayen bidiyon.

Rahotanni sun gano cewar gwamnan wanda yake a rikice yana gabatar da wasu shirye-shirye na k’aryata bidiyon ta hanyoyi da dama.

“Gwamnan yana cikin haɗari. Har yanzu yana Habuja inda yake neman hanyar tsira. K’ok’arinshi na sasantawa da ak’alla mutane uku da ke da faifan bidiyon shi ma ya ci tura. A yanzu gwamnan yana shirin ɗaukar hayar ‘yan gwagwarmayar bogi domin su soma yak’i a kan kafafan watsa labarai don su k’aryata bidiyon,” wata majiya da ta zaɓi kar a bayyana sunanta ta faɗa wa wakilin DAILY NIGERIAN.

Majiyar ta kuma ce akwai wani shiri na kai wa mawallafin DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar, farmaki sakamakon k’in sayar da bidiyon.

Leave A Reply

Your email address will not be published.