An Gano Masu Satar Shiga Runbun Ajiye Bayanan Jama’a A Facebook

0 332

Hukumar lura da aiyyukan kanfanoni na Birtaniya tana neman izinin chaje ofishin kanfanin “Cambridge Analytica” sakamakon bayana da aka samu na cewa, kanfanin ta samu shiga runbun bayanan masu amfani da Facebook fiye da Miliyan 50 million. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan majalisa a Amurka da kasashen Turai suka nemi sanin yadda wannan kanfanin da ta yi aiki dsa ofishin shugaban kasar Amurka Donal Trump a lokacin zabe ta samu daman shiga runbun bayanan jama’a.

A Amurka,’yan majalisa sun gauyaci shugaban kanfanin Facebook Mark Zuckerberg domin bayar da shaida a gaban ta. Hukumar Facebook ta bayyana cewa, ta yi hayan kwararen kanfanin binciken nan mai suna Stroz Friedberg domin gudanar da binciken kwakwaf na ko kanfanin Cambridge Analytica na rike da wasu bayanan jama’a zua yanzu. “Masu bincike daga Stroz Friedberg sun gudanar da bincike a ofishin Cambridge Analytica dake Landan da yammacin nan” “Ofishin watsa labarai na Birtaniya ya bukaci a sanar da bayar da takardar binciken kanfanin Stroz Friedberg domin gano gasikiyar lamarin” Kanfanin Facebook tayi asarar hanun jari kasha 7.0 ranar Litinin abin day a kawar da fiye da Dala Biliyan 40 a kasuwar jari sabosa masu zuba jari na fargabar cewa, wannan dokar zai iya bata sunan kanfain a idon duniya musamman masu hakar zuba jari.

“Lamarin fallasar ya fito fili a kan yadda Facebook ta kasa kare bayanan mutane, abin kuma ba zai yi wa Facebook kyau ba” inji Frank Paskuale, malami a jam’ar Maryland kuma Farfesa a harkar sharia wanda ya yi dogon rubutu a kan badakalar Silicon Balley. Haka kuma wani majiya ta shaida mana cewa, ranar Litinin wani shugaban bangaren tsaro na kanfanin Facebook ya shiurya barin aiki saboda rashin jituwar da ta tsakanin shi da saiuran masu gudanar da kanfanin a kan tsarre-tsaren sun a tattalin bayanan mutane. Daman shi yana da ra’ayin kawo karshen zargin da ake yinwa facebook na barin kasar Rasha ta yi kanekane a farfajiyar Facebook a lokacin zaben kaar Amurka, a zaben day a gudana a shekarar day a gabata.

Gidan jaridar c eta fara bayar da labarin barin aikin na jam’in amma facebook  ta ki ta ce komai da aka nemi bayanin ta. A wani sako twiter day a aika, Stamos bai karyata batun tafiyarsa ba amma y ace, “Duk da raderadin da ake yin a tafiya ta, ina nan ina gudanar da aiki na a kanfanmin Facebook sai dai lallai aikin da nake gudanarwa ya canza” Wanna badakalar Cambridge Analytica ya zama babbar kalubale ga mutuncin kanfaninfacebook dukk day a riga ya fadi sakamakon batun kasar Rasha, in da ake zargin kaaar Rasha ta yinamfani da facebook wajen fitar da labaran karya kafin da bayan zabe da aka gudanar na shugaban kasa a kasar Amurka a shekara 2016.

Kanfanin na Cambridge Analytica ta karyata dukkan zarge zargen da ka yi mata na goge dukkan bayanan da ta samu daga Facebook bayan ta amu labara cewa, bayana da ta samu na da kariyar doka a kan su bayan dokar shekarar 2014 da aka gabatar mata. An kara karfafa zargin da ake yi wa kanfanin Cambridge Analytica a bayana da wani maikacin gidan talabijan mai suna Channel ya yi ranar Litinin in day a samu wasu bayanai a sirance in da wasu manyan ma’aikatan Cambridge Analytica ke buga kirjin cewa suna iya canza sakamakon zaben kasashe ta hanyar murguda bayanai a kimiyance abin da ake ganin suna nufin zaben kasar Amurka ne da aka gudanar. Hukiumar Cambridge Analytica ta karyata zari da bayanan da Channel 4 ta gabatar suna mai cewa, bayana suna da matsaloli masu yawa, an kuma yi musu kwaslwarima tun daga magamgamun da aka yi da surutan da aka yi a cikin rahoton da suka gabatar.

Tuni Facebook ke fuskantar kira daga ‘yan majalisa tun lokacin da rahoton jaridar New York Times da na London’s Obserber suka fito a karshen mako. Sanata daga jam’iyyar Republican, John Kennedy ya bukaci Zuckerberg ya zo ya bayar da shaida a gaban majalisa, yayin da sanata dan jam’iyyar Democratic, Sanata Ron Widen ya aika da wakika ga Zuckerberg yabna neman ya bashai bayana yadda facebook ke gudanar da aikin sarrafa bayana da mutane suka ajiye a cikin runbun bayanan ta.

Hukumar Facebook kan aika lauyoyi ne su wakilceta a gaban majalisa ko kuma su aika kungiyar kwadago dana kimiyya da fasaha su wakilce ta a gaban ‘yan majalisun. Tuni dai kanfanin Facebook da sauran kanfaninin “social media” inrin su Twitter Inc da Alphabet Inc’s da YouTube da sauransu suka dauki matakin hana shiga harkar su daga kashen waje ta hanyar hana labarub karya da kuma kafa dokar yi musu katsalandan a harkokinsu. Ranar Litinin babban lauyan Connecticut ya ce zasu gudanar da bincike na musamman domin sanin ka’idoji da Facebook ke amfabi dasu wajen killace bayanan da mutane ke bata.

A na sa ran majalisar dattijai ta Amurka su mika daftarin gyaran dokar shashi 230 na dokar Communications Decency Act domin tsayar da hatkar safarar mata ta kafafen social,media da kuma yawaitar basta. Dokar dai ta riga ta wuce matakin farko a na saran ta zama cikakkiyar dokar nan bad a dadewa ba

Leave A Reply

Your email address will not be published.