An Gurfanar da Tsohon Gomnan Kano Ibrahim Shekarau da Tsohon Ministan Harkokin waje Aminu Wali a Gaban Kotu

0 260
Hukuma Mai Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Gurfanar da Tsohon Gomnan Kano Dr.Ibrahim Shekarau da Tsohon Ministan harkokin waje Ameenu Wali tare da Tsohon kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed, akan akan zargin Sun Amshi kudi Kimanin Naira million 950 Wanda wannan kudi Sun fito ne daga Hannun Tsohuwar Ministar Mai Diezani Alison-Madueke.
Alhamis 24th May,2018
Daga birnin kano Babbar Kotun Tarayya ta Gyadi Gyadi.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau tare da Tsohon Ministan harkokin waje Aminu Wali da kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed.
Mutanen da ake zargi sun gurfana a kotun cikin kamala kamar yadda aka saba ganinsu
Hukumar EFCC ta tuhumi jiga-jigan na jam’iyyar adawa da aikata laifuka shida.
Abinda ake tuhumarsu a kai
* Karbar kudi naira miliyan 950 daga uwar jam’iyyar PDP ta kasa
* Sun san cewa kudin bai fito ta halattacciyar hanya ba – halatta kudin haram
* Sun karbi kudin duk da suna da masaniya sun fito ne daga Tsohowar Ministar Mai  Alison-Madueke
* Ana tuhumar Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da ajiye kudin a wurinsu
* Sannan suka raba kudin
* Halatta kudin haram da hada baki.
Duka mutanen uku sun musanta tuhumce-tuhumce shida da aka yi musu da suka hada da karbar kudi daga jam’iyyar PDP a lokacin zaben 2015 duk da cewa sun san kudin ba ta halattacciyar hanya suka fito ba.
Bayanan da Shekarau/wali/Mansur suka yi shi ne an raba kudin ne domin gudanar da harkokin zaben 2015 ga yan Jam’iyyar PDP.
Sun ce an raba kudin ne ga shugabannin jam’iyya a dukkan matakan jihar kamar yadda kowacce jam’iyya ta ke yi.
Lauyoyin da ke kare bangarorin biyu sun kai ruwa-rana kafin daga bisani lauyan wadanda ake kara ya nemi belinsu.
Kuma ba tare da wata jayayya ba lauyan EFCC ya amince amma ya nemi a sauya sharudda masu karfi.
Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Mai shari’a Zainab Abubakar Bagi ta babbar kotu da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kano, ta bayar da belinsu a kan naira miliyan 100.
Bayan hutun dan lokaci, Mai Shari’a Zainab ta dawo inda ta bayar da belinsu akan kudin Da aka ambata da kuma samar da mutum uku da za su tsaya musu.
Daya daga cikin mutanen wajibi ne ya kasance ma’aikaci da ya kai mukamin darakta da kuma wanda ya mallaki babbar kadara a yankin da ke karkashin ikon kotun.
Sai a ranar 26 ga watan Yuni za a ci gaba da shari’ar.
Idan baku manta ba kwanaki kadan baya hirar Malam Shekarau, wanda dan takarar shugaban kasa ne a PDP ya yi hira da BBC, Da AIT Da kuma Gidan Talabijin na Liberty inda ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari.
Kafin fara zaman kotun miliyoyin mutane me suka cika hanyar zuwa kotun inda suka gabatar fa addu’a Ta musamman bayan jam’i Na sallah Da suka yi akan Allah ya taimaki jagororin Muna wannan shari’a.
kotun ta cika makil da magoya bayan Mal Ibrahim Shekarau dauke Da hotunan sa Da kwalaye Masu rubutu Na nuna goyon baya gare shi har sai da jami’an tsaro suka yi harbi sama da harba hayaki mai sa hawaye sannan aka tarwatsa jama’ar da suka taru a wajen kotun inda aka raunata mutane Da dama.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.