An Hana Ni Takara A PDP Don Na Ki Amince Ayi Lalata Da Ni – Fati Gombe

Fati Gombe

0 236

– Wata matashiya da ta nemi takarar majalisar jihar Gombe, Fati Gombe ta koka kan yadda wasu a jam’iyyar suka ki tantance ta

– Fati Gombe ta ce rashin amincewa ta bayar da kanta ga wasu gurbatattun jagororin jam’iyyar ya sa ba’a tantance ta ba

– Fati tayi ikirarin wani jigo cikin masu tantancewar ya bukaci da bayar da kanta gareshi ko ta bayar da toshiyar baki na N100,000 idan tana son a tantance ta.

  • An hana ni takara a PDP saboda na ki yarda ayi
  • amfani da ni – ‘Yar takarar majalisa a Arewa Source:
  • Twitter

Wata mai neman tikitin takarar majalisar jiha a Gombe a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hajiya Fati Gombe ta ce an ki tantance ta domin tsayawa takara a jam’iyyar ne saboda ta ki amincewa wasu gurbatattun shugabanin jam’iyyar suyi lalata da ita.

Fati Gombe wadda mawakiya ce ta bayyana cewar ta cika duk sharrudan takarar amma kwamitin masu tantance ‘yan takara tayi mursisi ta ki amincewa da takarar ta ba tare da wasu kwarararan hujjoji ba.

“Rashin tantance da kwamitin tayi bai bani mamaki ba saboda akwai daya daga cikin ‘yan kwamitin da ya bukaci in same shi a otal ko kuma in bayar da cin hancin N100,000 muddin ina son a tantance ni.

“Ina da shaida saboda lokacin da ya nemi in zo in same shi a otal din nayi amfani da waya ta na dauki maganar kuma nan gaba zan bayyana wa duniya wannan hirar kuma in fadi sunansa,” inji Fati.

Mawakiyar wadda ke da gidauniyar tallafawa mata, marayu da sauran marasa galihu da shawarci Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe da uwar jam’iyyar PDP suyi bincike tare da magance gurbatattun da ke jam’iyyar.

Souce :Naij Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.