An Kori Mourinho Daga Manchesters United
Mourinho ya fito aiki kafin a kore shi
Mourinho ya fito aiki da safiyar Talata bayan ya san cewa Manchester United za ta kori shi.
Abin da ya faru
Manchester ta kori Mourinho
Za a nada kocin rikon kwarya
Carrick zai jagoranci atisaye
Paul Pogba ya yi gaggawar goge sakon da ya tura a Twitter bayan korar Mourinho.
Mourinho ya bar Old Trafford
Manchester United ta raba gari da Jose Mourinho bayan shekara biyu da rabi yana horar da kungiyar.
Mourinho mai shekara 55, ya lashe kofin kalubale na Ingila da Europa League a Old Trafford.
Amma United tana matsayi na shida a teburin Premier, tazarar maki 19 tsakaninta da Liverpool da ke saman teburin kuma wacce ta lallasa Mourinho 3-1 a ranar Lahadi.
Manchester ta gode wa Mourinho tare da ma shi fatan alheri.
Mourinho ya horar da kungiyoyi a Portugal da Ingila da Spain da Italiya.
Ya lashe kofuna a kungiyoyin da ya horar a Porto da Real Madrid da Inter milan da Chelsea.
Sai dai kuma a Manchester United ya fuskanci kalubale duk da cewa ya lashe kofin kalubale da Europa League.
Amma wasu na ganin tun zuwansa ya kasa sauya abubuwa a Old Trafford.
‘Yan wasan da Mourinho ya saya a Manchester
Mourinho ya bar Manchester
Mourinho ya kashe jimillar kudi fam miliyan £358.8 wajen sayen ‘yan wasa tun zuwansa Manchester United.
Eric Bailly – Dan wasan baya – daga Villarreal – £30m
·Zlatan Ibrahimovic – Dan wasan gaba – daga Paris St-Germain – ya zo a son kansa
·Henrikh Mkhitaryan – Dan wasan tsakiya- daga Borussia Dortmund – £26.3m
·Paul Pogba – Dan wasan tsakiya – daga Juventus – £89m
·Victor Lindelof – Dan wasan baya – daga Benfica – £31m
·Romelu Lukaku – Dan wasan gaba – daga Everton – £75m
·Nemanja Matic – Dan wasan tsakiya – daga Chelsea – £40m
·Alexis Sanchez – Dan wasan gaba – Arsenal – musaya da Mkhitaryan
·Diogo Dalot – Dan wasan gaba – daga Porto – £19m
·Fred – Dan wasan tsakiya – daga Shakhtar Donetsk – £47m
·Lee Grant – Mai tsaron gida – daga Stoke £1.5m