An Saka Kungiyar Newcastle A Kasuwa

Newcastle

0 249

Mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Newcastle, Mike Ashley, ya bayyana cewa kungiyarsa ta Newcatle a kasuwa take saboda haka duk wanda yake bukatar siya zai iya zuwa ya tattauna kamar yadda lauyansa ya bayyana.

Sai dai wani tsohon mamallakin kungiyar, John Hall, ya tabbatar da cewa kungiyar zata iya kai matsayi da daraja irinta Manchester united saboda haka masu bukata suna bukatar suyi sauri. Mike Ashley, ya siyi kungiyar ne akan kudi fam miliyan 134 a shekara ta 2007 a hannun John Hall kuma a yanzu yana bukatar siyar da kungiyar ga mai bukata.

Lauyan Ashley ya ce, zai ziyar da kungiyar ne saboda yakasa goga kafada da kafada da kungiyoyi irinsu Manchester united da city da Chelsea wanda hakan yake ganin yakamata ya siyar da kungiyar domin bawa wasu dama. John Hall yace duk wanda zai siyi kungiyar yakamata ya kasha mata kudi adadin yadda ya biya ya mallaki kungiyar indai yana bukatar gogawa da manyan kungiyoyin gasar firimiya.

Mike Ashley dai yana bukatar siyar da kungiyar kafin watan disamba saboda wanda zai siya yasamu damar shiryawa kakar wasa mai zuwa da kuma kasuwar siye da siyarwa. Anyiwa dai kungiyar kudi fam miliyan dari uku da hamsin ga duk wanda yake bukata kuma tuni aka fara samun yan kasuwa daga kasar amurka sun fara tayawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.