An Yi Wa Mata 79, Maza 16 Fyade Cikin Watanni 7 A Kaduna

0 316

An Yi Wa Mata 79, Maza 16 Fyade Cikin Watanni 7 A Kaduna.


Cibiyar kula da wadanda aka yi wa fyade (SARC) dake jihar Kaduna ta bayyana cewa an shigar da kara da ya jibanci yi wa mata fyade har 95 a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli 2018.
Jami’ar cibiyar Juliana Joseph ta fadi haka a hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litini a Abuja inda ta kara da cewa bisa ga kararrakin da suka saurara a tsakanin wannan lokaci 16 daga ciki maza ne aka yi wa fyade.
” Cikin kararrakin fyade 95 da muka saurara 25 ‘yan shekara kasa da biyar ne, 28 kuwa ‘yan shekara 6 zuwa 10 sannan biyu masu shekaru 21 suwa 25.
” Gwaje gwajen asibiti ya tabbatar cewa mata biyu na dauke da ciki sannan 15 sun kamu da cututtukan sanyi.
Malama Joseph ta ce bisa ga bayanan da suka samu daga wajen wadanda aka yi wa fyaden sun nuna cewa 19 daga cikinsu makwabta ne suka yi musu fyade, bakwai kuma masu gadin gidajen su, 10 kums daga ‘yan uwa ne suka danne su.
” Wuraren da aka fi aikata wannan ta’asa a Kaduna sun hada da Tudun Wada, Kakuri Kudenden, Nasarawa, Hayin Banki, Gonin Gora, Dan Bushia, Romi da Rigasa.
A karshe Malama Joseph ta yi kira ga iyaye da su sa rika sa ido kan ‘ya’yan su.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.