An Yiwa ‘yan madigo bulala a bainar jama’a a Malaysia

0 384

An yi wa ‘yan madigo bulala a bainar jama’a a Malaysia

An samu wasu mata da laifin yunkurin yin madigo a cikin wata mota a kasar Malaysia, inda aka tsuttsula musu bulala a kotun Musulunci.

Matan biyu, Musulmi ne masu shekara 22 da 32, kuma an yi wa kowacce bulala shida a babbar kotun shari’a da ke jihar Terengganu.

Jami’ai sun ce wannan ne karon farko da aka kama wasu da laifin yin madigo sannan aka yi musu bulala a bainar jama’a.

Masu rajin kare hakkin dan Adam sun yi tur da hukuncin.

Dokokin Musulunci da na ‘yan-ba-ruwanmu sun haramta luwadi da madigo.

Wata jaridar kasar The Star ta ce fiye da mutum 100 ne suka halarci wurin da aka yi wa matan bulala.

Wata kungiyar kare hakkin mata ta Malaysia mai suna Women’s Aid Organisation ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ta yi “matukar kaduwa da samun wannan labari da ke keta hakkin dan Adam”. Sai dai wani jami’in hukumar zartara ta Terengganu, Satiful Bahri Mamat, ya kare matakin hukuncin, yana mai cewa sun yi wa matan bulala a bainar jama’a ne domin ya zama darasi ga wasu kuma ba da niyyar ji musu rauni ba.

A watan Afrilu ne hukumar Hisbah ta kasar ta kama matan, wadanda ba a bayyana sunayen su ba, bayan an gan su a cikin mota a wani dandali da jama’a ke zuwa a jihar Terengganu.

A watan jiya suka ki amincewa da aikata laifin inda kuma aka yanke musu hukuncin bulala da tarar N244,000.

Leave A Reply

Your email address will not be published.