An Zabi Wani Musulmi Ya Zama Kansila A America

0 238

Ikon Sai Kallo Musilmi Ya Zama Kansila A Kasar America

An zabi wani musulmi bahaushe dan asalin kasar Ghana a matsayin kansila a Majalisar Karamar Hukumar birnin Portland Maine da ke jihar Maine ta Amurka.

Zaben nasa na zuwa ne yayinda Musulmi da sauran baki a Amurkar ke ci gaba da nuna fargaba game da makomarsu a kasar bayan zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasa; saboda matakan da ya ce zai dauka na ko dai kora, ko na hana wasu shiga kasar.

A cikin wata hira da sashen Hausa na BBC sabon kansilan Pious Ali ya ce aikin da ya yi na baya a hukumar ilmi ta karamar hukumar ne ya taimaka wajen zabensa.

” (An zabe ni ne) domin mutane sun ga aikin da nake yi. Sun ga aiki na aiki ne na taimakon yara. Shi ya sa kowa na son mai taimakon yara.”

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.