Anyi Bikin Baiwa Sarkin Dukku Dake Jihar Gombe Sanda

0 202

An Yi Bikin Baiwa Sarkin Dukku Dake Jihar Gombe Sanda

Daga Adamu Usman Janhausa, Gombe

A yau Asabar Gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya baiwa Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Abdulkadir Haruna Rashid II sanda.

Gwamnan Dankwambo ya bayar da sandar ne kamar yadda al’ada ta tanada.

Taron ya samu halartar manyan baki kamar su Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi II, wanda amini ne ga Sarkin Dukku da kuma Mai Martaba Sarkin Bauchi Alh. Rilwan Suleiman da kuma Mai Martaba Sarkin Fika, Mai Martaba Sarkin Misau da Mai Martaba Sarkin Dass Alh. Usman Bilyamin Usman II da sauran Manya Sarakuna.

Da Kuma Dr. Aishatu Jibrin Dukku, Sanata Usman Bayero Nafada Da sauran ‘yan majalisun jiha.

Haka kuma mawaki Naziru M. Ahmad shi ma ya halarta.

Daga Karshe Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Abdulkadir Haruna Rashid ya yi Godiya Marar adadi ga Manyan Sarakuna da sauran Al’umma da suka Samu Halartan Wannan taro Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.