Anyi Garkuwa Da Wani Basarake A Katsina

0 129

Bayanai sun nuna cewa, an sace wani basaraken garegaji wanda shi ne dakacin kauyen Zandam dake karamar hukumar Jibia, mai suna Babangida Lawal, masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da shi. An sace baraken ne tare da wani dan kasuwa a kauyen mai suna, Murtala Rabe, yayin da masu garkuwa da mutane suka kai hari kauyen, uka kuma shi gidajensu inda suka yi awon gaba da su. Wasu daga cikin ‘yan kauyen da suka yi kokarin ceto su sun gamu da fushin ‘masu garkuwa d mutane don kuwa sun jima mutane da daman ciwo, a lokacin da suke kokarin yin haka. ya zuwa yanzu ba a samu bayanin neman kudin fansa ba daga masu garkuwa da mutanen Bayani ya kuma nuna cewa, a wani kauye dake kusa das u mai suna Gurbi Magarya, ‘yan ta’addan sun sace shanaye da dama. Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatarbda faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa, ‘yan sanda na kokarin ganin an ceto wadanda aka sacen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.