APC Zata Cigaba da Mulkin Nigeria Inji Mama Taraba

0 117

APC Zata cigaba da Mulkin Nigeria har Abada Inji Mama Taraba.

Ministar mata da harkokin cigaba, Sanata A’isha Jummai Al-Hassan ta bayyana cewa jam’iyyar ta ta APC zata kara karfi a zabe me zuwa domin zata kara cin sauran jihohin da bata ci ba a baya kuma a sama, watau shugaban kasa, APC ce zata cigaba da mulkin Najeriya har abada.
Da take hira da manema labarai ta bayyana cewa, za’ayi zaben jam’iyya na kasa baki daya kuma za’a yishi lafiya, ‘yan rikice-rikicen da ake samu a jam’iyyar nan da can ba abin tada hankali bane domin duk babbar jam’iyyar siyasa ta gaji haka.
Ta kara da cewa jam’iyyar tasu zata sake yin karfi a zabe me zuwa dan kuwa zata cinye jihohi irinsu Taraba, inda ta fito da Gombe, ta bayyana cewa zata sake tsayawa takarar gwamna a jihar, duk da cewa ita taci zabe a shekarar 2015 kuma suma PDP sun san cewa ita taci zabe amma da yake Allah beyi ita zata mulki jihar ba. Tace Amma in Allah ya kaita zaben 2019 da lafiya to zata sake tsayawa takarar gwamna kuma in Allah ya yarda zataci
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.