ASUU Na Neman Biliyan N220 Domin Janye Yajin Aikin Da Tashiga

0 103

Kungiyar malaman jami’a ta Najeriya, ASUU za ta ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani bayan ta kasa samun jituwa da gwamnati.

ASUU da ta shafe fiye da wata daya tana yajin aiki ta yi watsi da tayin gwamnati tarayya na biyan wasu daga cikin bukatun kungiyar.

Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya ta saki kudi kusan naira biliyan 15.4 domin jami’o’in na gwamnati.

Kuma Shugaba Buhari ya amince a biya malaman jami’oin kudadensu na ariyas naira biliyan 20 da suke bi daga 2009 zuwa 2002.

Sai dai kuma shugaban kungiyar malaman jami’o’in Biodun Ogunyemi ya yi watsi da kudirin na gwamnati kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mista Ogunyemi ya nuna cewa kudaden sun yi kadan daga cikin kudaden alawus da mambobin kudingyar suke neman gwamnati ta biya su.

Ya ce ya kamata gwamnati ta fayyace adadin kudaden da take nufi na malaman jami’oin da kuma hakkin na wadanda ba malamai ba don kaucewa rikicin da ya biyo baya a 2017 lokacin da gwamnatin da saki biliyan N22.9.

Shugaban malaman jami’o’in ya jaddada cewa biliyan N220 suke bukata daga gwamnati daga tiliyan 1.1 da suke bi.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki bayan kasa fahimtar juna tsakaninta da ministan ilimi Adamu Adamu kan bukatunta.

Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami’o’in, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatunta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.