ATIKU ABUBAKAR YA LASHE ZABEN FIDDA GWANI NA DAN TAKARAR SHUGABAN KASA A PDP, ZAI KARA DA BUHARI.

Atiku Abubakar

0 244

 

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin wanda zai kalubalanci shugaban Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a zaben da za a yi a watan Fabrairun 2019.

Alhaji Atiku Abubakar, ya samu tikitin takarar ne bayan ya samu nasara a kan abokan takararsa 11 wadanda su ma suka tsaya nemi tikitin takarar kujerar shugabancin Najeriyar a PDP.

Dan takarar shugabancin jam’iyyar na PDP, ya samu nasara ne da kuri’u 1532.

An dai gudanar da zaben ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers inda wakilai sama da 3,200 daga jihohin Najeriya 36 suka hallara domin zabar dan takarar da zai yi gogayya da shugaba Muhammadu Buhari.

Sauran ‘yan takarar da suka nemi kejarar shugabancin Najeriyar a jam’iyyar PDP, sun hadar da:

 • Jonah Jang da ya samu kuri’u 19
 • Datti Baba ya samu kuri’u 5
 • David Mark kuri’u 35
 • Turaki Taminu kuri’u 65
 • Sule Lamido kuri’u 96
 • Bafarawa kuri’u 48
 • Dankwabo 111
 • Ahmed Markafi kuri’u 74
 • Kwankwaso kuri’u 158
 • Olubukola Saraki kuri’u 317
 • Aminu Tambuwal kuri’u 693

Tuni dai sauran abokan takarar ta sa suka taya shi murna, inda tsohon shugaban majalisar wakilai na kasar Bukola Saraki ya yi magana a madadinsu.

Bukola Saraki ya ce ‘ Da ma muna sane da cewa dole ne a cikinmu mutum guda ne zai samu wannan takara, ya ce kuma a shirye suke su ba shi duk wani goyon baya domin samun nasarar jam’iyyarsu ta PDP 2019’.

Jam’iyyun siyasar ta Najeriya, sun kammala zaben ‘yan takararsu ne a yayin da a ranar Lahadin nan ne wa’adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta ba jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takara ke cika.

Leave A Reply

Your email address will not be published.