ATIKU Ne Kadai Ke Da madubin Ceto Nageria – Fati Muh’d

Fati Muhd

0 198

Shararriyar Jarumar nan ta Kannywood a masana’antar shirya fina-finan Hausa a zamanin baya watau Fati Muhammad ta Godewa Allah akan Nasaran da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya samu a zaben fidda Gwani da kayi a Jam’iyyar PDP.

Jarumar dai ta bayyana cewa ita a ra’ayin kanta tayi amannar cewa Atiku din shine kadai yake rike da mabudin ceton Najeriya daga halin da take ciki.

A kwanakin baya jarumar da ke ‘yar asalin jihar Adamawa ta samu matsayi a cikin wata gidanuniyar ta Atiku inda ta zama shugaba a sashen arewacin Najeriya. Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa a kwanan baya fitaccen dan siyasar ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC mai mulki inda ya koma jam’iyyar PDP ta adawa.

Jarumar dai tana ta kokarin Janyo hankalin yan wasan hausa akan su goyi bayan Atikun a zaben da za’ayi a 2019, acikin wadanda sukayi amanna da tafiyar da tsohon mataimakin shugaban kasar akwai JarumaMaryam Booth.

Leave A Reply

Your email address will not be published.