Atiku Ya Bada Gudunmawa Ta Bangaren Musulunci

0 272

GUDUNMAWAR ATIKU ABUBAKAR A FANNIN ADDININ MUSULUNCI ( kashi na 2)

Daga Abban Hajia

A Cigaba da bibiyar ayyukan alherin da Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ya yi wa addinin musulunci wanda cibiyar Atiku Hausa Media Center take yi, wanan cibiya ta sauka jihar Adamawa inda ta fara da garin Damare.

A cikin shekarar 2016 Alhaji Atiku Abubakar ya samarwa da Al’ummar garin Damare-Makama “A” dake Yola South katafaren masallacin Juma’a don kyautata Addinin su da yin ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

A zantawar walikin Atiku Hausa Media Centre ya yi da daya daga cikin mutanen garin mai suna Idrisu Aliyu Damare yace mun jima muna kokarin hada karfi da karfe wajen ganin mun samu masallacin juma’a a wanan garin namu don mu dinga yin sallar Jumma’a a ciki tare da koyar da ilimi addini ba sai mun tafi wani gari ba.

Katsam a tsakiyar shekarar 2016 sai ga Wazirin Adamawa yaji labarin abunda yake damun mu, cikin kankanin lokaci sai muka ga waziri ya aiko da kayan aiki aka gina mana wanan masallaci tare da zuba mana Qur’ani masu yawa da sauran littattafan Addini don koyar da Al’ummar musulmi.

Al’ummar garin nan kullum a cikin yima Alhaji Atiku Abubakar Addu’a suke don ganin ya samu nasara, cewar wani Dattijo malam Sani.

#AtikuHausaMediaCentre
#LetsGetNigeriaWorkingAgain

Leave A Reply

Your email address will not be published.