Atiku Ya Sharewa Masoya Buhari Hawaye A Abuja

0 176

Daga Abban Hajia

Wani Babban Jigo A Tallata Takarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Kira Ni. Wanda Ya Labarta Min Cewa, Korarren Dan Majalisar Wakilai A Jihar Kano Ya Kafa Kwamitin Tallata Buhari A Karkashin Inuwar Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari.

Babban Abin Takaicin Shine Ya Kwashi Masoya Buhari Daga Jihar Kano, da sauran jihohin Arewa Ba Kudin Mota (Transport)
Ba Wajen Kwana (Accommodation)
Sannan Ba Kudin Abinci (Feeding).

Wannan Ya Sa Aka Bar Su A Yashe, Suna Gararanba, Wane Tudu Wane Gangare, sai daya daga cikin su ya kira Rabiu Biyora akan a basu tallafi,nan da nan Biyora ya sanar da makusantan Atiku Abubakar akan wanann matsala. Nan da nan babu bata lokaci aka tura da motoci su dauko su don basu gurin kwana, abinci da kudin motar da zasu koma gida yaw.

Mutanen sunyi godiya sosai da fatan Alheri ga Alhaji Atiku Abubakar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.