Sananniyar ‘yar jaridar nan me yawan jawo cece-kuce kuma diya a gurin tsohon gwamnan jihar Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana sha’awarta da shiga addinin musulunci, tace babu abinda addinin kiristanci da take kanshi a yanzu ya jawo mata banda dimuwa da rudani.
Kemi ta bayyana hakane a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada Zumunta da muhawara inda ta sanya hotunan ta sanye da Hijabi sannan ta rubuta cewa:
Kwanannan zata karbi addinin musulunci, kuma a da ta kasance tare da kakarta wadda ta rasu tana da shekaru dari da biyu a Duniya, makarantar da take zuwa kusa da gidan kakartane shi yasa ta koma can da zama, su kanyi sallah sau biyar a rana ba sau daya a sati ba kamar yanda take yi tare da shaidanun mutane yanzu ba, tace, suna shagulgulan sallah babba da karama tare.
Tace Musulunci addinine na zama lafiya kuma a cikinshine zata samu nutsuwa.
Ta dai karkare zancenta da cewa, yanzu babu ruwanta da addinin kiristanci, dan kuwa babu abinda ya tsinana mata a rayuwa banda rudani, musulunci zata koma kuma duk wanda baya son addinin musulunci sai ya dena bibiyarta da lamurranta, komai yana da lokaci dama, yanzu dai ta tabbata cewa a addinin musuluncine zata samu nutsuwar da take nema.
https://arewarulers.com/sitemap.xml
Iam the CEO/Founder Of ArewaRulers.com | Mukhtar Ismail Muhammad By Name...
No Comments
Leave A Reply
Cancel Reply
Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Up up Islam
Gud thinking, may Allah help you to Achieve your goals
Allahu Akbar.
Allah Akbar
Allahu AKbar May Allah guide u to be among d successful Muslims