Baya ta haihu: Sabon Jirgin saman Najeriya na iya shiga gundumemiyar matsala

0 140

Baya ta haihu: Sabon Jirgin saman Najeriya na iya shiga gundumemiyar matsala.

– Murnar dawowar Jirgin saman Najeriya na iya fuskantar matsala

– Ma’aikatan tsohon kamfanin Jirgin sama na kasa sunyi barazanar hana shi fara aiki matukar ba’a biyasu hakkokin da suke bin bashi ba

Kungiyar ma’aikatan zirga-zirga ta jiragen sama (NUATE) ta ce zata hana sabon kamfanin Jiragen Nigeria Air fara aiki har sai biya tsofaffin ma’aikatan na Nigeria Airways hakokkinsu da aka rike na tsawon shekaru 14 wanda aka yi jumulla ya kai zunzururtun kudi Naira biliyan N45b.

Sai dai ministan harkokin jirage sama na kasa Hadi Sirika ya bayyana cewa sabon kamfanin ba shi da wata alaka da tsohon kamfanin Jiragen na kasa da ma’aikatan suka yi aiki. Ministan ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a cikin karshen makonnan, inda ya ce “Kamfanin Nigeria Air ba shi da wata alaka da kamfanin Nigerian Airways, saboda kowanensu daban yake gudanar da ayyukansa”. “Ban san akan me suke korafi ba, saboda in har akwai wanda ya damu da halin da suke ciki bai wuce minista ba kuma ina da yakinin sun fahimci hakan”.

Jim kada bayan kammala taron ganawa da manema labarai, Olayinka Abioye wanda shi ne sakataren kungiyar ta NUATE ya ce sun bayar da wa’adin ranar 31 ga watan Yuli don a biya su kudinsu, ko kuma gwamnati ta fuskacin fushin su.

Ya kara da cewa shuwagannin kungiyar sun gana da minista Hadi Sirika a lokuta daban-daban domin nemawa tsoffin ma’aikatan hakkinsu tun bayan daina aiki da kamfanin yayi a watan Satumbar shekara ta 2004.

 Abioye ya cigaba cewa, in har zata iya kirkirar wani kamfani da sunan cigaba da yiwa kasa aiki, to, tabbas ya kamata a biya ma’aikatan da suka yiwa kasarsu hidima na tsawon shekaru da dama, wanda wasu daga cikinsu sun dade da rasuwa ba tare da an biya su kudadensu ba.

Sannan ya bayyana cewa, zuwa yanzu kungiyar tana da ‘ya’ya sama da 2000 wanda suke tsumayin hakkinsu.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.