BUHARI – Me Zan Cewa Kanawa Idan Suka Tambaye Ni Me Yasa Gwamnansu Ya Ke Karbar Cin Hanci Yana Murmushi?

0 203

Tsohon Sanata Bashir Garba Lado wanda yana daga cikin ‘yan kwamitin tallan takarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo shawara a wani zama da suka yi cewa, me zai hana jihar Kano da Legas su zama waje na karshe da Shugaban Kasa zai ziyarta bisa la’akari da yawan Al’ummar su?

“Yaya kuma idan mutanen jihar Kano suka tambaye ni dalilin da ya sa Gwamnan su ya ke karbar cin hanci yana murmushi?” Buhari ya fada yayin amsa tambayar Lado.

“Maganar gaskiya ba ni da amsar wannan tambaya. Ba zan iya zuwa Kano yakin neman zabe ba, sai dai idan hakan ya zama dole”. Buhari ya kammala bayar da amsa yayin da mahalarta taron suka dauki tafi gami da yaba masa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.