Buhari Zai Dauki Matakin Akan Faifan Bidiyon Karbar Kudin Ganduje

0 257

Buhari Zai Dauki Matakin Akan Faifan Bidiyon Karbar Kudin Ganduje

Dan-gani Kashe nin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano, Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya jaddada cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Sha Alwashin daukar mataki akan bidiyon da aka dauki wani Gwamnan APC yana karbar cin hanci da rashawa a hannun ‘yan kwangila.

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne aka gani a wannan bidiyon.

Sannan Tarin ‘yan kwangilar da suka tattauna da jaridar DAILY NIGERIAN k’ark’ashin yarjejeniyar k’in ambatar sunansu sun ce gwamnan da kansa yake amsar cuwa-cuwar kashi 15 zuwa 25 na kowanne aiki da aka gabatar a jihar.

“Buhari ya ga bidiyon wani Gwamna yana karbar cin hanci, ya kuma yi alkawarin daukar mataki a kansa”.

Danbilki ya bayyana haka ne a gidan Rediyon Rahama dake jihar Kano ta hanyar wayar salula.

Leave A Reply

Your email address will not be published.