Chanza Jam’iyya Ba Tserewa EFCC Ba ne – Ibrahim Magu

Ibrahim Magu Shugaban EFCC

0 229

Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa ‘yan siyasa da ke ficewa daga wannan jam’iyya zuwa waccan, ba alamomi ba ne da ke nuna cewa sun tsere wa EFCC daga gurfanar da duk wani cikin su wanda ya wawuri dukiyar gwamnati.
Da ya ke jawabi a wurin wata ganawar musamman da ya yi da editocin wasu jaridun kasar nan a Lagos, Magu ya ce babu wurin buya ga irin wadannan ‘yan siyasa, ballantana su fake daga kamu da, bincike da kuma gurfanarwar da EFCC za ta yi musu.

“Kotu ce kawai za ta iya wanke mutun daga zargin ko ya ci kudi ko bai ci ba. Idan ya ci za ta hukunta shi, idan bai ci kudi ba kuwa, za ta sallame shi.”

Da ya ke maida martani daga wata tambaya da aka yi masa cewa jam’iyyar APC mai mulki na yin katsalandan a cikin aikin EFCC, Magu cewa ya yi, bai taba samun wani umarni ko koron yin wata alfarma kan wani bincike ya hukumar sa ke yi ba.

Magu cewa ya yi abin ya zama tamkar al’ada ga ‘yan siyasa idan ana binciken su sai su rika cewa ana yi musu bi-ta-da-kulli na siyasa.

” Ina ganin saboda siyasa ta matso, shi ya sa duk wani motsi da EFCC ta yi, sai a jingina shi da siyasa.” Inji Magu.

Ya ce kafafen yada labarai na da hakkin a kan su kada su bari batagarin ‘yan siyasa su yi amfani da dukiyar da suka sata ta hanyar jan ragamar gwamnati irin yadda suka ga dama.
Magu ya kara yin kira ga editocin kada su bari jaridun su su zama kafafen da wadanda suka wawuri dimbin dukiya wurin yin kukan munaficci.

Ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu, kusan kashi 10 bisa 100 kacal na dukiyar da aka wawuce a baya aka fallasa. Daga nan sai ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara bada muhimmanci ga yaki da cin hanci da rashawa.

Ya ce akwai bukatar bankuna su kara karfin sa-ido da kulawa da abin da ke faruwa a cikin bankunan su.
Ya kuma roki Babban Bankin Najeriya, CBN ya sake gyara ka’idojin tsaftace ayyukan bankunan ‘yan kasuwa, domin ta haka ne kawai inji shi za a iya kasa karfin cin nasarar yaki da cin hanci da rashawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.