Cikin Rashin sani Jama’a Ke Raina Sana’ar Daukan Hoto – Hauwa

Hauwa Idris Saidu

0 309

Hauwa Idris Sa’idu ta ce ta fara harkar daukar hoto bayan ta kammala karatunta na sakandire bayan ta sami wasu kayawenta na sana’ar daukar hoto wanda hakan ya ja hankalinta har ta fara a matsayin sana’a.

Matashiyar ta ce tana daukar hoto ne mafi lokutan da ake biki ko party na yara sannan wasu lokutan takan raka kawayen nata wajen sha’ani na biki ko wani babban taro inda take rike masu kayan aiki inda take lura da yadda suke gudanar da aiki.

Hauwa ta ce ta fara daukar hoto ne da karamar kyammara kirar Cannon, wani lokacin ma tana daukar hotonne da wayar salula har ta kai ga samun babbar kyammara.

Daga karshe ta bayyana cewa tana matukar son sana’ar daukar hoto yanzu haka ita da ‘yar uwarta sun fara sha’awar bude gidan daukar hoto a Maiduguri, sannan ta ce da dama mutane na yi wa masu daukar hoto kallon sana’ar su ba sana’a bace mai girma ba harma akan raina wa sana’ar ta su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.