Cristiano Ronaldo Zai Dawo real Madrid
Bayan da aka raba jadawalin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League a ranar Litinin ta kungiyoyi 16 da za su buga zagaye na biyu, Juventus za ta ziyarci Atletco Madrid.
Hakan na nufin Cristiano Ronaldo wanda ya bar Real Madrid a kakar bana zuwa Juventus, zai je Madrid birnin da ya buga tamaula kaka tara a Santiago Bernabeu.
Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Juventus a wasan farko a ranar 19 ga watan Fabrairu a filinta na Wanda Metropolitano.
Juventus ta yanke shawarar zuwa Spaniya a ranar Litinin 18 ga watan Fabrairu domin yin atisaye, wanda hakan ne zai bai wa Ronaldo damar wasa a birnin tun barinsa Real.
Kungiyar ta Italiya ce ta yi ta daya a kan teburin rukuni na takwas da maki 12, ita kuwa Atletico ta hada maki 13 a rukunin farko a mataki na biyu biye da Borussia Dortmund.