Da Dumi-Dumi Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sake Sanya Dokar Hana Fita Ta Awa 24 Jihar

0 136
A ranar Talata ne Gwana Nasir El-Rufai ya jagoranci taron majalisar tsaro ta jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sake sanya dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24 a garin Kaduna da kewaye a ranar Juma’a.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook.

Hakazalika ya ce dokar ta shafi garin Kasuwan Magani da Kajuru da Katari da kuma Kachia kuma ta fara aiki ne daga karfe 11 na safiyar Juma’a.

Kakakin gwamnan ya ce an dauki matakin ne bayan kashe wani barasake HRH Agom Adara a ranar Juma’a wanda aka sace a makon jiya.

Daga ya bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu,inda ya ba da tabbacin hukunta wadanda suka aikata hakan.

A ranar Laraba ne aka sassauta dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24 a garin Kaduna zuwa sa’o’i 13.

A ranar Litinin da dare ne gwaman ya sanar da mutanen jihar cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan a yayin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai.

Amma akwai rahotannin da ke cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 26.

Hakazalika ya ce an kama mutane da adama da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin.

Ya kuma ce za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin tayar da wannan hatsaniyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.