Dalilan Aisha Waziri Umar Fitowa Takarar Majalissar Tarayya

Aisha Waziri Umar

0 290

Dalilan Aisha Waziri Umar Fitowa Takarar Majalisar Tarayya

Daga Wakilinmu

Fiatacciyar Lauya, kuma gogaggiyar ma’aikaciya, Aisha Waziri Umar ta fiton neman amincewa takarar Majalisar Tarayya, a zaben 2019 main zuwa, domin ta wakilci Karamar Hukumar Jere ta Jihar Barno.

Cikin wani daftari tsare-tsaren manufofin ta, ta bayyana matsalolin da jihar Barno ke ciki sanadiyyar hare-haren Boko Haram, ta kuma nuna rawar da za ta raka idan aka zabe ta a Majalisar Tarayya.

Da ya ke ta na da Gidauniyar tallafa wa masu karamin karfi, musamman kananan yara da harin kunar bakinn wake ya jikkata, Aisha ta bayyana cancantar ta ta wakilcin wannan karamar hukumar da ta ce za ta kai su ga samun ci gaba sosai, har ma da jihar baki daya.

“Kamar yadda ka sani, Jihar Barno ta kasance jihar da hare-haren ta’addancin Boko Haram ya yi wa katutu a yankin Arewa-maso-gabas a Najeriya. Illar kunar-bakin-wake da sauran munanan hare-hare ta haifar da matsanancin halin kuncin rayuwa ga al’ummar wannan yanki, bisa la’akari da dimbin rayukan da suka salwanta, tun daga barkewar rikicin zuwa yau.

“A matsayina na mai kishin Najeriya da nuna damuwa kan halin da mutanen Jihar Barno suka tsinci kansu a ciki, na kasance mai matukar nuna alhinin irin wannan halin kuncin rayuwar. Kan wannan dalili ne ya sanya na cimma matsaya, ina mai kaskantar da kai, tare da daukar aniya. Shi ya sa na sadaukar da kaina don hidimta wa al’umma idan aka zabe ni na zama ’yar Majalisar Wakilai ta Taraya mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Jere.

“Kasancewar na taba yin fafutikar ayyukan jinkai a lokacin da musifar kunar-bakin-wake ta kai makura a yankin Arewa-maso-Gabas, tun daga shekarar 2012, ina da cikakkiyar masaniya da fahimtar rikirkitattun al’amurran da suka kawo matsalar rayuwa ga mutanen Jihar Barno.

“Don daukar matakin shawo kan matsalolin, na kafa kungiyar da ba ta gwamnati ba, wato Gidauniyar Imara ko ‘Imara Foundation’ a Turance, don tallafa wa rayuwar wadanda suka jikkata sanadiyyar hare-haren kunar-bakin-wake, musamman mata da kananan yara. Tun farkon kafuwar Gidauniyar ta kawo dauki ta hanyar gudanar da shirye-shiryen kyautata zamantakewar al’umma, inda kacokam aka tunkari harkokin ciyarwa, musamman samar da abinci mai gina jiki da ilimi da horon sana’o’in bunkasa tattalin arziki da kuma samar da kudaden shiga ga al’umma.

“Baya ga kyautata rayuwar mutanen karkara da gogewa ta a harkokin kula da rayuwar al’umma, fannin ilimin da nake da kwarewa a kai, shi ma wani makami ne da ke da kyakkyawan tasirin samar da wakilci nagari ga al’ummar Mazabar Jere a Majalisar Tarayya, musamman kan harkokin da ke bukatar jawo hankalin gwamnati a matakan tarayya da jiha don tunkarar matsanancin halin rayuwar al’umma cikin gaggawa.

“Sannan na kasance abokiyar hadin gwiwar rubuta littafin bin kadin aikin lauya a Najeriya – babban littafin a ake amfani da shi wajen nazarin aikin lauya da dalibai ke yi a Najeriya. A daidai lokacin da na gudanar da aikin rubuta kudurorin da ake gabatar wa Majalisar Dokoki, al’amarin da ya ba ni damar sanin makamar aikin Majalisar Dokokin kasa.

“Wasu daga jerin dokokin da na rubuta an tabbatar da su har sun zama doka a matakin tarayya da jiha, kuma sun hada da: Dokar kafa Hukumar kula da noman rani da ta albarkatun ruwa, da Dokar da ta kafa Hukumar Samar da Irin Shuka ta Kasa da dokar da ta kafa Hukumar Kula da Ayyukan Killace Dabbobi ta Kasa. Wadannan kudurori sun hada da Hada-hadar sufuri a Kaduna da Hukumar Kula da Rumbun Tara Hatsi ta Kasa.

“Baya ga ayyukan lauya da na jinkai, na kasance mai fafutika wajen yada ilimi na musamman (ilimin nakasasu) a Najeriya. Na kafa Cibiyar Kula da Yara Masu Bukata ta Musamman a Abuja. Wannan kuwa wata makaranta ce ta musaman da ke kula da ilimantar da yara masu bukata ta musamman; wato masu nakasa ko fama da wahalhalu wajen koyon karatu.

“Bisa la’akari da al’amuran da aka jero a sama, ina da kwarin-gwiwar jin cewa zan iya isar da koken al’ummar Mazabar Jere ta Tarayya, tare da daukacin al’ummar Jihar Barno.

Kudirorin Da Nake Fatan Cimmawa a Majalisar Tarayya:

*Bijiro da sababbin dabaru wadanda za su yi tasirin warware matsalolin da ke kawo tarnakin ci gaban al’umma da suka dabaibaye Jihar Barno, musamman al’amarin da ya jibinci sauyin yanayi da rashin aikin yi.

*Zan zama mai magana da yawun talakawa da wadanda ake kai wa farmaki da mutanen da ake zalunta, a daidai lokacin da na ke fafutikar tabbatar da jagoranci nagari da zai samar da daidaiton adalci a zamantakewar rukunin mutanen da ke tattare da hadarin kai wa farmaki, musamman mata da marayu da nakasassu.

*Zan tabbatar da ganin Majalisar Tarayya ta kafa dokokin da za su warware matsaloli don biyan bukatun mutanen da na ke wakilta.

“Dangane da shirin zaben shekarar 2019 da ke karatowa, ina neman tallafin kudi da kuma neman amincewar ka, don ci gaba da gangamin yakin neman zabe a yankunan karkara. Domin tallafin ka zai yi tasirin samun kuri’u, tare da goyon bayan masu zabe a Jihar Barno, ta yadda za a kai ga samun kyakkyawan sakamako a wannan zabe.”

#Rariya

Leave A Reply

Your email address will not be published.