Dalilan da suka sa ni fita daga PDP zuwa PRP – Takai

0 215
Dan takarar gwamna a jihar Kano Salihu Sagir Takai ya ce sun fice daga PDP ne sakamakon rashin adalci da ke gudana a jam’iyyar.
Dan siyasar wanda a baya aka bayyana a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar PDP, yanzu kuma ya sanar da barin jam’iyyar zuwa PRP.
A makon da ya gabata ne dai ta bayyana cewa Abba Kabir Yusuf wanda bangaren Kwankwasiya ke ra’ayi aka tsayar a matsayin dan takarar jam’iyyar ta PDP a Kano, ba Malam Salihu Sagir Takai ba.
Wannan ne kuma dalilin da ya sa Takai ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar PRP.
Takai ya ce rashin adalci da nuna son kai ne suka dabaibaye PDP a Kano.

 

“Mun wayi gari a PDP ana yin abin da aka ga dama ba tare da an tafi da ‘yan jam’iyya ba,” in ji shi
Uwar jam’iyyar PDP ce dai ta tattaro shugabannin jam’iyyar na jihar inda suka zauna suka tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a matsayin dan takarar gwamna, yayin da kuma bangaren da ke yi wa tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso biyayya ya gudanar da zabe kuma ya tsayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna.
Daga baya ne dai uwar jam’iyyar ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takararta na gwamnan a Kano.
Ana dai ganin Sagir Takai ya tafi jam’iyyar PRP ne domin ta tsayar da shi dan takararta na gwamna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.