Dalilin Da Yasa Bamu Baiwa Buhari Sakamakon WAEC Ba A 2015 – WAEC

WAEC Buhari

0 158

Dalilin Da Yasa Bamu Baiwa Buhari Sakamakon WAEC Ba a 2015 – WAEC

Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga gaba da sakandire, WAEC ta yi bayanin dalilin da ya sa ta gaza baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon jarrabawarshi a shekarar 2015.

A shekaranjiya Juma’a ne dai hukumar ta mika wa Buhari sakamakon jarrabawar ta shi ta hannun rajistran hukumar, Iyi Uwadiae a fadar gwamnatin tarayya.

Toh sai dai wannan lamari ya haifar da cecekuce daga wasu bangaren, inda ‘yan Nijeriya da dama ke tambayar wai shin hukumar me ya sa bata baiwa shugaban sakamakon jarrabawar ba a 2015, tun da dai ya na hannunta?.

Da ta ke maida martani game da wannan batu, hukumar ta ce ta yi haka ne saboda a 2015, wata kungiya mai suna Move On Nigeria ita ta je Ghana inda ta bukaci hukumar ta fitar da sakamakon.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta tambayi wai shin a Ghana ne aka zana jarrabawar?

“Domin gudun tamtama, wanda ya zana jarrabawa da kotu kadai ne za su iya bukatar sakamakon jarrabawa” Inji hukumar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.