Dalilin Da Yasa Bana Son Auren Mai Kudi – Jamila Nagudu

0 625

Jarumar dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Jamila Umar Nagudu, ta bayar da dalilan da yasa bata son auran namiji mai kudi.

Jamila a wani shiri na Kannyflix ‘Mujallar Tauraruwa’ tace babban dalilin da yasa bata son auran mai kudi shine saboda ba zai samu dama da lokacin tattali da tarairayarta ba.

Amma da aka juyo Kan batun irin mijin da take son aure ,Jamila tace “Bana son auran miji mai arziki, haka kuma bana son auran miji talaka”. “Ina so na auri mutumin da zai dauki nauyin bukatuna ciki harda samun lokacin zama tare dani. Bana son miji mai tarin dukiya da yawa saboda yawan harkokinsa ba zasu bari ya samu lokaci na ba,” inji ta.

Jamila ta fito a fina finai da dama kamar irin su Miji Da Mata, Wani Gari da kuma Jamila Da Jamilu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.