Dalilin Da Yasa Dole Na Zubar Da Hawaye – Atiku Abubakar

Dalilin Da Yasa Na Zubar Da Hawaye - Atiku Abubakar

0 232

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa babban dalilin da yasa ya fashe da kuka a wajen amsar fom din takara da wata kungiya ta siya masa shine tuna irin halin da aka shiga a kasa Najeriya.

Wata kungiyar matasa kuma masoya tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ne suka hada taro sisi suka siya masa fom din takarar shugabancin Najeriya.

Matasan sun bayyana cewa sun yi wa Atiku haka ne saboda nuna masa irin goyon baya da muradin sa da suke yi.

Shugaban kungiyar Adekemi-Adesanya Eboda, ya roki Atiku da ya yi na’am da wannan himma na su ya fito domin ceto Najeriya daga bakin mulkin APC da ake fama dashi a kasar nan.

A na shi jawabin Atiku ya bayyana cewa a tsawon shekarun sa a siyasa, bai taba sauraron jawabi daga bakin wani matashi da ya sosa masa rai, ya tada masa hankali, ya cika shi da tausayi kamar yadda jawabin Etoda ya yi masa ba.

” Wannan abu da kuka yi mini ba zan manta da shi, kuma ina tabbatar muku cewa tare duk za mu yi wannan tafiya tun daga zaben fidda dan takara har zuwa na kasa baki daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.