DaliliNa na Dawowa Harkar Fim inji Zainab Indomie

Zainb Indomie

0 527

Jarumar ta daina fitowa a fim yayin da tauraron ta ke haskawa sai dai kamar yadda ta bayyana dalilin faruwar haka shine don ta ba yan baya damar damawa a masana’antar kannywood.
Hirar ta da BBC tauraruwar ta kuma karyata rade-raden da ake yi a kanta na rshin ganin fuskar ta a fim.

Tana mai cewa “A kowanne lokaci ana son wani ya bai wa wani dama don shi ma ya samu lokacin damawa, don in da ina tsaye a kan karagata da ban bai wa ‘yan baya dama ba”.

Tace ta dawo bakin aikin ta gadan-gadan kuma idan ta daina kuma toh a sani cewa aure ne yayi sanadin yin haka.

“Na dawo bakin sana’a ta wadda In Allah Ya yarda idan aka ga na koma to sai dai idan aure ne”, inji Indomie.

Sai dai ta ce a yanzu ba za ta iya cewa ga fim din da za a soma ganinta a cikinsa ba, sai dai ana tuntubar ta kuma a cikin wannan watan ma akwai shirin fim da take aiki a kan shi.

Jarumar wacce tayi murnar zagayowar ranar haihuwar ta cikin makon nan ta samu tarba daga abokan sana’ar ta da masoya inda suka yi mata lale-maraba bayan ta sanar da dawowar ta.

Fitattun jarumai Adam A.Zango da Ali Nuhu suna daya daga cikin abokan sana’ar ta da suka wallafa hotunan ta don taya ta murna dawowa masana’antar fim.
Ta kuma jaddada dangantakar dake tsakanin ta da jarumi Adam A.Zango tsabani jita-jitan da ake yi na cewa suna soyayya.

Ni na dauki Adamu ubangida na ne kuma kamar dan uwa na dauke shi kamar yadda ya dauke ni amma babu komai tsakani na da shi.

“Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana’a” ta bayyana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.