Dan Najeriya Ya Lashe Gasar Cin Abinci Mai Mugun Yaji A Kasar Chana

0 186

Jaridar China Daily ta ruwaito wani dan Najeriya da bata bayyana sunansa ba a matsayin wanda ya lashe gasar cin abinci mai mugun yaji a kasar ta China.

Ita dai wannan gasa mutane daga kasashe biyar ne suka shiga domin gwada sa’arsu ta cinye wani dandakakken nama mai dankaren yajin barkono.

Sai dai kuma dukkab wadan da suka shiga gasar sun gaza cinye abincin yayin da shi dan Najeriya ya cinye ya kuma sude kwanon. An karrama dan Najeriyar da yaci gasar da lambar yabo.

Leave A Reply

Your email address will not be published.