Dan Nayiwa Atiku Abubakar Murna Lashe Zabe Ai Ba Laifi Bane – Adam A Zango

Adam A Zango

0 191

Shahararren mawaki kuma jaruma a fina-finan Hausa na Kannywood Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Adam A Zango ya bayyana cewa ba laifi bane don ya taya alhaji Atiku Abubakar murnar lashe zaben cikin gida na jam’iyar PDP da yayi.
Wannan martani dai na zuwa ne bayan da jarumin ya dora hotan taya murna wa dan takarar shugaban kasar a shafinsa na sadarwar zamani na Instagram.

Sai dai hakan ya sanya jama’a na ta cece kuce akan yiwuwar ko cewa jarumin ya koma bayan Atiku ne, wanda a zaben baya yana kan gaba wajen nuna goyon baya ga shugaba Muhammadu Buhari.

Biyo bayan cece-kucen ne jarumi Adam Zango ya wallafa wani hoto na shugaba Buhari a shafinsa na instagram inda yake kara jaddada ma jama’a cewa har yanzu yana tare da shugaba Buhari dari bisa dari.
“A nan nake, kamar yadda na fada a baya, ba biya akayi nake goyon bayan Buhari ba. Ra’ayi na ne, wanda hakan bazai hanani yiwa dan PDP murna ba muddun ina da alaka da shi.” inji jarumi Adam Zango.

Akwai wasu daga cikin yan wasan kwaikwayon da tuntuni sun nuna goyon bayansu ga Alhaji Atiku Abubakar wanda wasu daga cikinsu ma akwai masu yi masa campaign. Daga ciki akwai irinsu Fati Muhammad da Kuma jarumi Al-amin Buhari.

©arewamobile.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.