Dan Wasan Nigeria “Ahmed Musa” ya Fitar dasu kunya

0 174

Dan Wasan Nigeria Ahmed Musa ya Pitar dasu Kunya.

Kwallo biyun da Ahmed Musa ya zura a minti na 49 da 75 sun bai wa Najeriya damar da doke Iceland da ci 2-0 a gasar kofin duniya.
Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar hada maki uku bayan wasa biyu.
Kuma a yanzu ita ce ta biyu a rukunin bayan Croatia wacce tuni ta kai mataki na gaba bayan da ta doke Argentina da ci 3-0 a ranar Alhamis.
A yanzu Ahmed Musa shi ne dan kwallon da ya fi kowanne ci wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ya zura hudu.
Najeriya za ta kara da Argentina a wasan ta karshe na rukunin D domin fayyace kasar da za ta bi Croatia domin zuwa zagayen kifa-daya-kwala ‘yan 16.
https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.