Dan Wasan Super Eagles ‘Ahmed Musa’ da Matar sa JulietSun Samu Karuwa

0 221

Dan Wasan Super Eagles ‘Ahmed Musa’ da Matar sa JulietSun Samu Karuwa.

Image result for ahmed musa and wife

Kwana daya bayan yin nasara zama dan wasa na 8 da kwallon sa yafi birgewa a gasar kofin duniya na wannan shekaru, Ahmed Musa da Matar sa Juliet Ejue sun samu karuwar da
.
.
Dan wasan wanda tauraron sa ke haskawa ya sanar da wannan abun farin ciki a yammacin ranar alhamis a shafin sa na Instagram
.
.
Ya rubuta “Ina mai sanar daku cewa cikin dan kanakanin lokaci da ya wuce a baya Allah ya albarkace ni da samun karuwar yaro. Kalamai baza su iya bayyana irin farin ciki dake tattare dani ba
.
.
Ya rubuta hakan ne tare wallafa hoton jaririn da suka samu
.
.
Wannan shine da na uku da dan wasan super eagles zai samu kuma na farko auren sa da amarya Juliet Ejue
.
.
Dan wasan ya haifi yara biyu Ahmed Musa Junior da Halima Musa auren sa da tsohuwar uwardakin sa Jamila
.
.
Kwallon sa shine na uku a cikin jerin kwallaye da aka ci a gasar kofin duniya na FIFA

Wannan abun farin ciki ya biyo bayan wanda ya samu na zama dan wasa mai kwallo mafi birgewa na 8 a gasar kofin duniya na wannan shekarar
.
.
Kwallon shi na biyu wasan Nijeriya da Iceland a gasar ya fito takarar jerin kwallaye mafi birgewa sai dai amma bata yi nasarar zama na daya ba
.
.
Dan wasan kasar Faransa wacce tayi nasarar zama zakarun gasar Benjamin Pavard shine ya lashe kyautar gasar
.
.
Ahmed Musa shine dan wasan mafi kwallo a tarihin yan wasan tawagar Nijeriya a gasar kofin duniya. Ya samu wannan matsayin ne samakon kwallaye biyu da zura a raga a gasar bana wanda ya daga yawan kwallayen shi daga biyu zuwa hudu
.
.
Auren sa da Juliet Ejue

Dan wasan kungiyar Leicester ya auri amaryar shi Juliet cikin shakarar 2017 bayan rabuwar sa da Jamila. Bikin auren su ya samu halarci manyan jarumai a dandalin wasan kwallon kafa da harkar nishadi
.
.
Anyi bikin a garin mahaifan amaryar sa dake nan Ogoja dake jihar Kuros Riba.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.