Di Maria Na Son Komawa Gasar Firimiya

0 222

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG dan kasar Argentina, Angel Di Maria, yana son komawa kasar Ingila domin yaci gaba da buga wasa idan kwantaraginsa ya kare da kungiyarsa.

Di Maria mai shekara 30 a duniya yana tunanin barin kungiyar PSG  a karshen wannan kakar sakamakon kwantaraginsa yazo karshe sannan kuma ya na son komawa gasar firimiyar Ingila.

Sai dai albashin da dan wasan yakeso ya dinga karba ne yayi yawa kuma da yawa daga cikin kungiyoyin gasar firimiya bazasu iya biyan albashin fan dubu dari biyu ba a duk sati. Wakilin dan wasanne dai yakeson dan wasan yakoma kasar Ingila da buga wasa kuma a kwai kungiyoyi da dama daga kasar Ingilan da suke son daukar dan wasan wanda ya taba bugawa Real Madrid wasa.

Dan wasan ya taba zaman shekara daya a Manchester United a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Luis Van Gaal, dan kasar Holland bayan da United din ta siyo shi daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

A kwanakin baya ma dai an danganta dan wasan da komawa kungiyar Jubentus da Barcelona da kuma kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya sannan kuma kungiyar Boca Junior ma ta kasar Argentina tanason dan wasan yakoma gida domin yaci gaba da buga wasa.

#Leadership

Leave A Reply

Your email address will not be published.