Dole Real Madrid Ta Nemi Neymar Tinda Ta Kare musu – Inji Messi

Messi and Neymar

0 336

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi ya bayyana cewa abin bakin cikine kan wasa Neymar yakoma Barcelona ganin yadda kan wasan yabuga wasa a kungiyar ta Barcelona kuma ya lashe kofuna da dama tare dasu.

Neymar yakoma PSG daga Barcelona a watan Agustan shekarar data gabata akan kuki fam miliyan 200 wanda hakan yasa a yanzu kan wasan yafi kowanne kan wasa tsada a duniya kuma ya lashe kofin kasar Faransa.

Messi yace Neymar ya lashe manyan kofuna da suka haka da gasar zakarun turai da gasar Laliga da kuma ragowar kofuna saboda haka har yanzu akwai Barcelona a zuciyarsa kuma idan yakoma Real Madrid zai kara musu karfi.

“Tabbas nasar Real Madrid zasu nemi Neymar sabida ya iya kwallo kuma duk wani abu da ake bukata a wajen kan kwallo Neymar yanadashi kuma irinsa Real Madrid take nema”

Messi yace yana bakin cikin ganin Real Madrid ta kara karfi saboda bayason ganin su suna lashe kofuna kuma idan har Neymar ya koma kungiyar zasu cigaba da cin kofuna da kafa tarihi kala-kala.

Sai dai yace baya ganin Real Madrid zata buga abin kirki a wannan kakar bayan kungiyar ta siyar da Cristiano Ronaldo zauwa Jubentus duk da cewa har yanzu kungiyar batayi rashin nasara ba a wasanninta na laliga bayan buga wasanni uku

Har ila yau Messi yace yana ganin Barcelona zata iya sake lashe kofin laliga da kuma kofin zakarun turai wanda sukayi shekaru huku basu kauka ba sannan kuma ya ce yana fatan kungiyar zata bawa maraka kunya a wannan kakar.

A karshe kuma ya bayyana cewa baya gasa da Ronaldo saboda kowa abinda yakeyi daban kuma gashi yanzu Ronaldo yabar kasar ta Sipaniya zuwa Jubentus ta kasar Italiya.

#Hausaleadership

Leave A Reply

Your email address will not be published.