Duk lokacin da nake so zan iya shiga Kano – Inji Tsohon Gomnan Kano Rabiu Musa Kwankwanso

Duk lokacin da nike so zan iya shiga Kano>>Kwankwaso

0 267
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, a duk lokacin da ya bushi iska zai iya shiga garin Kano ba tare da neman izini gun kowa ba.

 

An jima dai ba’a ga Kwankwaso a bainar jama’a a Kano ba, kuma akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar Kano na yanzu, Dr. Andullahi Umar Ganduje da Kwankwason wadda ta fito fili lura da irin kalaman da suke jifar junansu dashi.
Jaridar Rariya ta bayyana cewa Kwankwason yanzu yace baya bukatar neman Izini kamin ya shiga Kanon.

Leave A Reply

Your email address will not be published.