Farashin Taba Sigari da Giya ya tashi Dalilin karuwar Haraji akan su

0 169
Giya da Tara Sigari zasu kara kudi tsada dalilin karuwar Harajin su.
Farashin lemuka nau’in giya da kuma taba sigari zai karu bayan amincewa da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi na gyara da aka yi wa dokar haraji.
Tun a kwanakin baya ne ministar kudi Kemi Adeosun ta rubutawa shugaban kasar wasika inda ta nemi amincewarsa domin a sake d’aga harajin.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Lahadi, sabon harajin zai fara aiki daga ranar 4  ga watan Yunin shekarar 2018.
A sanarwar Adeosun ta bayyana cewa sabon kudin harajin za a raba shi zuwa shekaru uku domin sai-saita illar da hakan zai kawo kan farashin kayayyakin.
Ministan ta ce sabon karin harajin zai kara samarwa da gwamnati kudaden shiga kuma zai sa a rage ta’ammali da kayayyakin saboda illar da suke da shi ga lafiya.
Karakashin sabon harajin kowanne karan sigari za a kara masa ₦ 1, a shekarar 2018 kenan a kowane kwali za a kara ₦20. A shekarar 2019 zai karu zuwa ₦40 a kowanne kwali ya yin da a shekarar 2020 za zama ₦58.

https://arewarulers.com/sitemap.xml

Leave A Reply

Your email address will not be published.