Fati Niger Za Ta Fitar Da Sabon Kundin Wakokinta (Album) Na 2018

Fati Niger

0 418

A yanzu haka dai shiri ya yi nisa a game da wakokin da fitacciyar mawakiya Fati Niger ta ke yi na fitar da sababbin wakokinta a kundin adana wakoki wato album na shekarar 2018 daga nan zuwa karshan wannan shekarar da muke ciki. Kundin waka wanda ake sa ran zai dauki wasu wakoki na musamman har guda 6 kuma zai bambanta da sauran wakokin da mawakiyar ta saba yi a baya ta fuskar inganci da kuma tsari domin kuwa, an dauki dogon lokaci ana shiri da kuma nazarin yadda tsarin wakokin da kuma shi kansa kundin wakar zai kasance daidai da tsarin wakokin da suke tafiya a wannan lokacin, don haka ne ma ake ganin wannan aikin zai dauki lokaci kuma zai ci kudi mai yawan gaske.

An dade dai ba a ganin kundin wakokin Fati Niger a kasuwa, domin kuwa tun wanda ta ya mai suna ‘Yargata a shekarar 2012 ba ta sake yin wani ba sai a wannan lokacin da take yunkurin fito da wannan a matsayin kundin wakokinta na 2018.

A can baya dai ta yi kundin wakoki masu yawan gaske na ji kuma da na kallo, amma dai daga 2012 zuwa yanzu ba ta yi wani kundin waka ba, wanda hakan kamar yadda Fati Niger ta fada yana da alaka da tsayawa da ta yi tana godon nazari don ta zo da wani sabon salo na wakokin da za ta burge masu sauraron ta, kuma a yanzu tana ganin lokaci ya yi da za ta fito da basirar ta ta domin ta zama amsa ga masu sauraron ta.

Mun tambaye ta ko tsawon lokacin da ta dauka ba ta fito da kundin waka ba, ta ci gaba da wakoki? Sai ta ce, “Sosai ma ina yin wakoki na siyasa da na biki da kuma tallace-tallace na kamfanoni domin ka san ban tsaya a waje daya ba, don shi mawaki yana rikida ne a koda wanne lokaci, kamar yanzu da yake lokacin siyasa ne sai muka koma ga harkokin siyasa, don haka ita wakar siyasa ba lallai bane ka ji ana sayar da ita a kasuwa ba sai dai ka ji a gidajen rediyo haka su ma wakokin biki ba ko ina zaka ji su ba.”

Da yake an samu tsawon shekaru saboda kina yin wakokin amma ba ki yi wani kundi na adana su ba, kina ganin haka ba zai sa a nemi wasu wakokin a rasa ba?

Sai Fati Niger ta ce, “To ni dai ina ganin hakan ba zai zame matsala ba, domin kuwa na ci gaba da wakoki na da suka shafi siyasa, aure, tallace-tallace da sauransu. Kuma abin alfahari ma shi ne lokaci zuwa lokaci na kan samu lambobi na karramawa akan wakokin da na ke yi to ka ga hakan ba wani abu ne da zai shafi basira ta ba, domin ita baiwa ce da Allah ya bani, kuma duk da haka ina da tsari da na ke adana wakokina domin gudun bacewar su, kuma hakan ya sa na samu kwarewa ta fuskar adana wakokina, sai dai kamar na siyasa da na biki ai ka ga na lokaci ne ba sai lallai ka ajiye su ba don lokacin su zai iya wucewa, haka su ma wakokin biki. Amma ganin tsawon lokacin da masu sauraron wakokina musamman album ba sa ji na shi ne ya sa a yanzu na kudiri yin aikin sabon kundin wakata na 2018 daga nan zuwa karshan shekara don haka masoyana ina yi musu albishir da fitowar wakoki na nan gaba kadan, kuma zan ba su mamaki a fagen waka fiye da yadda suka sanni a baya saboda wakokin da zan fito da su ni kaina ina kallonsu a matsayin na musamman don kuwa ba don basira ta Allah ba ce, da sai na ce na kure basira ta a wadannan wakokin. To amma da yake kayan Allah ne ba zan ce na kure ba na san zai bani wadda ta fi ta yanzu nan gaba in dai muna da rai da lafiya, amma kawai abin da zan ce da masoyana wadannan wakokin da zan yi daban suke, don ba a saba jin su ba kuma a kalla fitowa ta farko za su kai guda shida kafin sauran su biyo baya, wadanda za su hada da na sauraro da kuma na kallo.

Da yake duniyar fasaha ta ci gaba an samu sauyi wajen tallatawa da kuma sayar da wakoki da finafinai ko, akwai wani tsari da Fati Niger za ta fito da shi wajen sayar da wakokin ta a yanzu? Sai ta ce “Ai yadda zamani ya zo a haka za ka tafiyar da kasuwancin ka don haka ni ma zan tafiyar da tsarin tallata wakokina da kuma sayar da su ta hanyar da zamani ya ke tafiya a yanzu don haka duk wata kafa ta online da ake bi ana tallata kaya domin isar da su ga masu bukata zan bi hanyar kuma nan gaba kadan ma za a fara ji da gani don haka masoyana ina yi muku albihsir da tallace-tallace da zan fara na wakoki na nan gaba kadan a kafofin sadarwa na zamani, don haka ina yiwa masoyana fatan alaheri a duk inda suke kuma su ci gaba da saurarona za su ga sabon kundina na wakar 2018 a karshen shekarar nan da izinin Allah.

Leave A Reply

Your email address will not be published.