Gamayyar Kungiyoyi Sun Siyawa Ganduje Form din Takarar Gomna

Gomnan Kano Dr.Abudullahi Umar Ganduje

0 267

A yau Litainin ne Kungiyar ‘One2Tell10 Buhari Support Group – Kano Chapter’ karkashin Coordinator din ta na jihar Kano wato Engr. Jazuli Abdulkarim Daiyabu da Sakataran ta na kasa Yuguda Abdul Aziz, Sun jagoranci sauran kungiyoyi wajen mikawa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje fom dinsa na takara. Wanda hadakar kungiyoyin suka saya masa.

Wadannan kungiyoyi ne dake mara baya ga shugaba Buhari da gwamnan Kano Ganduje, kuma sun mika wannan fom din da kudin sa ya kai kudi kimanin naira miliyan 22,500,000 wanda aka saya a ofishin jam’iyyar APC ta hannun shugaban ta na jihar Kano Alh. Abdullahi Abbas da sauran shugabanni.

Leave A Reply

Your email address will not be published.