Ganduje Ya Aika Wa Sheikh Daurawa Sammaci Saboda Yayi Huduba Akan Bidiyon Badakalarsa

0 244

A daren jiya Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sa aka cikumo Kwamandan Hisba na jihar wanda yayi Hudubar juma’a akan faifan bidiyon Gwamna da aka nuno shi yana karbar dalar Amurka.

Rahotanni sun tabbatar da cewar Gwamnan ya sa an kamo dukkan Malaman da suka yi huduba akan bidiyon zuwa gidansa dake titin Miyangu a daren jiya dan jin dalilinsu na yin huduba kan badakalar tasa.

Bayanai sun nuna cewar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana a cikin hudubarsa da yayi a Masallacin Ansarus Sunnah dake unguwar Fagge cewar wannan video ya Isa shaida idan idan mutum yana neman hujja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.