Ganduje ya nada sabon mataimakin gwamna

Nasiru Yusuf Gawuna Kwamishinan Aikin Gona

0 253

Gwamnan Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Nasiru Yusuf Gawuna a kan mukamin mataimakin gwamna.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce Gwamna Ganduje ya mika sunan “Nasiru Yusuf Gawuna ga majalisar dokokin jihar Kano ranar Litinin a matsayin mutumin da yake son zama mataimakin gwamna.”

Yanzu haka Gawuna shi ne kwamishinan aikin gona kuma sau biyu yana rike mukamin shugaban karamar hukumar Nasarawa da ke cikin birnin Kano.

Gwamna Ganduje ya nada sabon mataimakin gwamna ne makonni kadan bayan saukar Farfesa Hafizu Abubakar, wanda ya yi zargin cewa rayuwarsa tana cikin hatsari.

Daga bisani, Farfesa Hafizu, wanda yaron siyasar tsohon gwamna Sanata Rabi’u Kwankwaso ne, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar inda ya koma PDP – jam’iyyar da uban gidansa ya koma.

Gwamna Ganduje dai shi ne ya zama mataimakin gwamna tsawon shekara takwas da Sanata Kwankwaso ya yi gwamnan jihar.

Sai dai manyan ‘yan siyasar biyu sun fada rikicin siyasa tun bayan zaben shekarar 2015, wanda jam’iyyar APC ta lashe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.