Gaske Ne Rasuwar Sani S.K?

0 402

Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Sani Garba SK. ya musanta labarin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa.

A ranar Litinin ne wasu mutane da ke amfani da shafukan sada zumunta suka yi ta baza labaran karya a kan cewa ya rasu bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Ya bayyana cewa har ya gaji da amsa wayar tarho domin irin yawan mutanen da suke kiransa domin su ji ta bakinsa a kan ko da gaske ya mutu.

Amma dai tauraron ya ce yana fama da ciwon suga kuma ya gano hakan ne cikin ‘yan kwanakin nan da ya je asibiti.

A baya dai an yada labaran karya a kan mutuwar wasu fitattun taurarin Kannywood, ciki har da Sadiya Gyale da Sani Moda.

BBCHAUSA

Leave A Reply

Your email address will not be published.