Gomnatin Kano Zata Aurar da Mata Zawarawa Dubu Uku 3000

0 161

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamiti mai mambobi 23 wadanda zasu dauki nauyin aurar da zaurawa da matan da basu taba aure ba dubu 3 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Mohammed Garba ne ya sanar da hakan a jiya Laraba.

Garba ya ce, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya amince da kafa kwamitin wanda da zai fara aiki nan take. Limamin babban masallacin jihar Kano Farfesa Sani Zahraddeen ne zai jagorancin mambobin kwamitin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.