Hadarin Shaye Shayen Maye Ga Al’umma Nasihar Falalu Dorayi (karanta kaji)

0 193

HANKALI yana cikin abu da ake fara gwada Dan adam dashi a Mu’amala rayuwa. Yayin da ya zama abin lalatarwa a gurin wasu matasa maza da mata a zamanin nan da muke ciki.

Bayan mun sani an karantar damu matsalar GIYA, CACA, da BAUTAR GUMAKA an hAda su cikin AYAH guda sobada Illarsu ga Dan Adam, SHAIDAN yana amfanin da hakan wajan saka mana KIN juna da gaba, sannan ya shagaltar damu ga barin ambaton Allah da yin bauta gareshi.

ANNABI (SAW) Ya fada mana,
“Duk abin da ke gusar da hankali a matsayin GIYA yake, kuma ko wacce irin giya an haramta shanta, Kuma duk wanda ya mutu yana shan giya ko abin da ke gusar da hankali, bai tuba ba, to bazai shaki kanshin giyar ALJANNA ba.” A wani hadisin na Anas
RASULULLAH (SAW) Yace;
“Allah ya la’anci mutane goma akan ababen maye,
Wanda ya sa’antata,
Wanda yasa a sa’antata.
Wanda ya sha,
Wanda yai dakon ta,
Wanda akaiwa dakon,
Wanda ya bayar,
Wanda ya sayar,
Wanda ya ci kudin,
Wanda ya saya,
Wanda aka sayarwa.
Dukkan su Allah ya la’ance su

Shaye shaye yai nisan da duk bama tunani cikin alummar musulmi, cikin Dalibai, Jami’an tsaro soja da Yansanda,
Maaikatan gwamnati, Yan siyasa direbobi, Leburori, Yan mata, Samari, matan aure, Entertainment industry, Yan kasuwa, manoma da sauransu.

Shi yasa sai kanka ya kulle idan kaje yawan makudan kudin da wani ma’aikacin ko Dan siyasa ya sata na Al’umma. Kai kasan ba aikin hankali bane.

Muyi laakari sosai da yadda kisan kai ya zama abin sauki, FYADE kuwa tun daga yara yan shekara 3 har shekara 18, 20 abin da yai sama babu wanda ta tsira, garkuwa da mutane kullum ne sai wanda Allah ya tsare, Kuma shaye shaye ne yake ta sarrafa hankulanmu.

A Karshen shaye-shaye dai a cikin uku ne. Ko ka kare rayuwa a gidan Mahaukata a daure kamar mahaukacin kare, ko ka fada komar Yan sanda alkali ya tura ka gidan yari. Ko ka mutum ya mutu cikin maye yaje su hade da Mala’iku mummunar cikawa.

Allah ya shiryemu ka tsaremu cikin dukkan mummunan aiki.

Juma’at Kareem.

Leave A Reply

Your email address will not be published.